Labarai
Ba mu sauya dokar haraji da majalisa ta sahale ba – Fadar Shugaban Najeriya

Fadar shugaban kasa ta musanta zargin cewa ta sauya sabbin dokokin haraji a sirrance, bayan da ta ce babu wani gyara da ta yiwa dokokin wanda majalisar tarayya ba ta amince da shi ba.
Wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, da dan takarar shugaban kasa na jamiyyar LP a zaben da ya gabata, Peter Obi tare da wasu kungiyoyin fararen hulla suka bukaci a dakatar da aiwatar da dokokin.
Da ya ke zantawa da manema labarai, hadimin shugaban kasa kan kafafen yada labarai, Mr Temitope Ajayi ya ce babu wata sukar yan adawa da za ta hana aiwatar da dokokin a watan Junairu.
Ya ce har yanzu babu wata hukuma da ta fito fili ta yi zargin cewa an sauya dokoki, inda ya bayyana masu yada zarge-zargen a matsayin yan adawa dake kokarin haifar da ruɗani kan manufofin gwamnatin.
You must be logged in to post a comment Login