Labarai
Ba ni da niyyar barin Jam’iyyar NNPP- Sanata Kwankwaso

Ɗan takarar shugaban ƙasa a zaben da ya gabata na shekarar 2023 karkashin jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce ba shi da niyyar barin jam’iyyar, duk da cewa a shirye yake ya tattauna da sauran ‘yan siyasa kafin zaɓen 2027.
Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bayyana hakan ne a taron kwamitin zartaswa na ƙasa da aka gudanar a Abuja, inda ya bayyana NNPP a matsayin “amaryar siyasar Najeriya” mai cike da manufofin ci gaba da kula da al’umma.
A nasa bangaren, sakataren jam’iyyar na ƙasa, Dipo Olayoku, ya ce NNPP na da shiri sosai domin tunkarar zaɓen gwamnan jihar Anambra wanda za a gudanar a watan Nuwamba 2025 da kuma zaɓen kananan hukumomin Abuja a Fabrairu 2026.
Jam’iyyar ta kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi rijista da hukumar INEC domin samun katin zabe, tana mai jaddada cewa kujerar ku ita ce muryarku.
You must be logged in to post a comment Login