Connect with us

Labarai

Aminu Gurgu Mai Filo ya fice daga PRP zuwa NNPP

Published

on

Sakataren yaɗa labaran jam’iyyar PRP na Kano Alhaji Aminu Gurgu Mai Filo ya fice zuwa jam’iyyar NNPP.

Hakan na cikin wani saƙon murya da ya aike wa Freedom Radio.

Mai Filo ya ce, “Mun zo mu taya Malam Ibrahim Shekarau ya maimaita kujerarsa, da yardar Allah kuma Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya zama shugaban ƙasa”.

Alhaji Gurgu Mai Filo ya yi kira ga ƴan Najeriya da su rungumi jam’iyyar NNPP domin tseratar da ƙasa.

Wannan dai na zuwa ne ƙasa da mako guda da tsohon Gwamna Malam Shekarau ya tsallaka jam’iyyar ta NNPP tare da magoya bayansa.

Jagoran jam’iyyar na ƙasa tsohon Gwamna Kwankwaso ya ce, suna maraba da kowa a jam’iyyar.

Watanni biyu kenan da tsohon Gwamna Kwankwaso ya ɗauko jam’iyyar ta NNPP wadda a yanzu take zaman jam’iyya ta biyu da yawan ƴan majalisu a Kano.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!