Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Nishadi

Ba ruwana da daukakar mahaifina gwara na tsaya da kafata – Dan Akshey Kumar

Published

on

Jarumi Akshey Kumar ya bayyana cewa dansa Aarav ya zabi ya tsaya ya dogara da kansa ba wai ya jingina da daukakar mahaifinsa jarumi Akshey Kumar ba. Akshey Kumar yace dan sa Aarav baya kaunar a rika dangantashi da daukakar mahaifinsa Akshey Kumar kasan cewar shi ya zabi ya tsaya da kafafuwansa bawai da mahaifinsa ba.

A cewar jarumi Akshay kumar tabbas ya goyi bayan kalaman dan nasa Aarav, yana mai cewa dama tun asali dansa na daban ne ba kamar sauran ‘ya ‘yan jaruman masana’antar shirya fina fina ta Bollywood ba.

Akshey kumar yace ” Kamar dai yadda kowa ya sani a wannan duniyar mutane da dama suna tunkaho da kudi ko daukaka ta mahaifinsu maimakon suma suyi kokarin kafa kansu kamar yadda mahaifansu sukayi.

Aarav dai da ne ga jarumi Akshay kumar da kuma matarsa jaruma Twinkle Khanna kuma an haifi Aarav ne a shekarar 2002 kuma bayanshi suna da ‘ya mai suna Nitara mai shekaru bakwai yanzu haka a duniya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!