Labarai
Ba za mu bari Najeriya ta rushe a hannun mu ba – Shattima

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, ya ce gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ba za ta taba bari Najeriya ta rushe a hannunta ba, duk tsananin kalubalen da ake fuskanta.
Shettima ya bayyana haka ne yayin bikin yaye daliban Cibiyar Nazarin Manufofi da Muhimman bukatu ta kasa NIPSS da ke Kuru.
Ya ce gazawar Najeriya ba wai matsala ce ga kasar kadai ba, har da al’ummar duniya baki daya.
Shettima ya kara da cewa ya sha fada wa wasu jami’an diflomasiyya cewa duniya za ta fi samun kwanciyar hankali idan Najeriya ta dore.
A cewarsa, tarwatsewar kasar zai iya haifar da kaurar ‘yan Najeriya masu kwazo sama da miliyan 50 zuwa kasashen Turai, lamarin da zai shafi kowa a duniya.
You must be logged in to post a comment Login