Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

*Ba za mu lamunci cin zarafin da aka yi wa shugaban kungiyar ASUU ba – Jami’ar Bayero*

Published

on

Kungiyar malaman jami’o’i ta kasa ASUU reshen jami’ar Bayero a Kano, ta nuna rashin jin dadinta da yadda wasu jami’an tsaron na DSS suka ci zarafin shugaban kungiyar Farfesa Abdulkadir Muhammad.

Wannan na cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugabanta Farfesa Haruna Musa da kuma sakatarenta Dr Yusuf Umar Madugu.

Sanarwar ta ce lamarin ya faru a ranar 18 ga wannan watan Agusta da ya gabata inda jami’an DSS din suka tare shi a kan titi a nan Kano lokacin da suke tafiya suna jiniya, suka lalata masa mota sannan suka ci zarafinsa.

Haka zalika kungiyar ta bukaci hukmar ta DSS ta gudanar da bincike a kai don hukunta wadanda ake zargi da cin zarafin shugaban na su, tare da kiyaye aukuwar hakan a nan gaba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!