Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ba zamu lamunci karin farashin man fetur ba – NASU

Published

on

Kungiyar ma’aikatan jami’o’i da ba malamai ba, NASU ta ce, ba za ta Amince da karin kudin man fetur ba, wanda aka kara daga Naira dari da Ashirin da uku zuwa Naira dari da Arba’in da uku digo tamanin ba.

Ta cikin sanarwar da kungiyar ta fitar mai dauke da sa hannun sakataren ta Peter Adeyemi.

Sanarwar ta ce, karin ba ya cikin tsarin da ya kamata abi a wannan lokaci da duniya ke fuskantar annobar corona.

Peter Adeyemi ya kara da cewa, kungiyar ta lura da yadda tattalin arziki ya samu kansa a ciki, sakamakon cutar corona wanda ya sanya ‘yan kasar nan cikin mawuyacin hali.

Kungiyar ta bukaci gwamnatin tarraya da ta sake nazartar farashin man fetur din, duba da halin matsi da ma’aikata da sauran ‘yan kasa ke ciki.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!