Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Rudunar sojan ta kasa ta musanta sojoji 356 za su ajiye aiki

Published

on

Rundunar sojin kasar nan ta musanta labarin da ake yadawa na cewar sama da sojoji 356 sun ajiye aiki sakamakon rashin samun kulawa da ya sanya ba su da sha’awar aiki.

Ta cikin sanarwar da rundunar ta wallafa a shafin ta na Twitter ta ce labarin da wasu jaridun internet ke wallafawa bashi da tushe ballantana makama.

Sanarwar ta kara da cewa labarin na bayyana cewa akalla sojoji 356 ne suka ajiye aiki sakamakon yadda aikin ya fita a ransu saboda rashin kulawa, sai dai rundunar ta ce wannan na zuwa ne dai-dai lokacin da rundunar ke kara aikewa da jami’an ta sassan kasar nan don yaki da ta’addancin kungiyar Boko Haram.

Rundunar sojin ta cikin sanarwar ta yi All…. Wadai da labarin, inda ta ce abinda rundunar ta sa ni shi ne wasu daga cikin jami’an ta na shirye shiryen yin ritaya sakamakon karewar wa’adin aikin su.

Kazalika rundunar ta ce a yanzu haka ta kara aikewa da rundunar sojoji zuwa arewa masu gabashin kasar nan yayin da wasu da dama aka rarrabasu zuwa sassan kasar nan don yaki da ayyukan ta’addanci.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!