Labarai
Ba zan bari yan ta’adda su mamaye kowacce ƙaramar hukuma ba- Gwamna Zulum

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bayyana cewa ba zai taɓa bari ‘yan ta’adda da masu tayar da ƙayar baya su mamaye kowace ƙaramar hukuma a jihar sa ba.
Gwamnan ya bayyana hakan ne bayan wata ganawa da suka yi da shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, a fadar shugaban ƙasa da ke birnin tarayya Abuja, inda suka tattauna kan ƙalubalen tsaro.
Yayin tattaunawar dai, Gwamna Zulum ya shaida wa shugaban ƙasa halin da yankin musamman ma jihar Borno ke ciki dangane da matsalolin tsaro.
Zulum da Shugaba Tinubu sun tattauna yadda gwamnatin tarayya da ta jihar za su haɗa kai domin shawo kan matsalar tsaro da ke addabar yankin.
You must be logged in to post a comment Login