Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Zulum ya tabbatar da mutuwar mutane 81 da ‘yan ta’adda suka kaiwa hari

Published

on

Gwamnan Jihar Barno Farfesa Babagana Umara Zulum ya tabbatar da kashe mutum 81 da yan ta’addar Boko Haram suka yi bayan mamaye kauyen Faduma Koloram dake karamar hukumar Gubio ta jihar ta Borno a jiya talata.

Gwamna Babagana Umara Zulum ya bayyana hakan ne lokacin da ya kai ziyara gurin da aka kai harin domin jajantawa wadanda suka tsira.

Gwamna Zulum yace mutum sha uku sun samu raunuka lokacin da suke kokarin guduwa.

Sanna yace mutum arbain da tara daga cikin tamanin da dayan da aka kashe an riga an binne su kafin zuwan sa garin inda 32 biyu yan uwan su suka dauke su.

Daga nan Gwamna Babagan Zulum yace yan ta’addar da suka kai hari karamar hukumar Gajiram a kwanakin baya sune dai suka kai harin karamar hukumar ta Gubio sannan suka kashe mutum 81.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!