Labarai
Ba zan biya N60,000 ga masu amfana da shirin N-Power ba
Gwamnatin tarayya ta ce baza ta biya Naira dubu sittin ba a matsayin kudaden fita ga matasan da suka amfana da shirin N-Power kamar yadda suka bukata.
A jiya ne dai wasu daruruwan matasa suka yi wata zanga-zanga a zauren majalisar kasa, da nufin jan hankalin gwamnatin tarayya don basu Naira dubu sittin-sittin da takardar daukar aiki, sa’annan da bukatar Ministar harkokin jin kai da ci gaban al’umma Sadiya Umar Farouk ta sauka daga mukamin ta.
Sai dai cikin wata sanarwa da mataimakin daraktan yada labaran ma’aikatar Rhoda Shaku Iliya ta fitar, ta ce gwamnatin tarayya za ta kashe biliyoyin kudi don ci gaba da shirin ga sauran matasa da za a dauka nan gaba kadan.
Sanarwar ta kara da cewa, bukatar ta su bata cikin tsarin shirin na N-Power tun da fari, kuma Gwamnatin bata yi wannan shiri ba na sallamar wanda suka amfanar da adadin kudin da suka bukata.
A saboda haka ma’aikatar ta ce Gwamnatin tarayya ta ce baza ta biya kudin da suka tasamma Naira biliyan dari uku ga dimbin matasa a matsayin kyauta ba.
You must be logged in to post a comment Login