Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ba zan sauka daga kujera ta ba – Gwamna Masari ga kungiyar CNG

Published

on

Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya yi watsi da bukatar gamayyar kungiyoyin kare martabar Arewa ta CNG na ya sauka daga mukamin sa.

Gamayyar kungiyoyin reshen jihar sun bukaci masari ya sauka daga mukamin sa, sakamakon kalaman da ya yi na cewa kowa ya kare kan sa daga harin yan bindiga.

Da yake mayar da martani kan kiran, Masari ya bayyana shi a matsayin rashin hankali, sakamakon rashin fahimtar da suka yi wa kalaman sa.

Bayanin hakan na cikin wata sanarwar da mai bai wa Masari shawara kan harkokin yada labarai Alhaji Abdul Labaran ya fitar.

Idan za a iya tunawa gwamnan Masari ya umarci al’ummar jihar da su dauki matakin kare kan su daga harin yan bindiga, lokacin da ya kai ziyarar ta’aziyya a Jibia.

Wannan ne ya bai wa gamayyar kungiyoyin dama na yin kira ga gwamnan da ya sauka daga mukamin sa, a matsayin sa na babban jami’in tsaron jihar sa kuma yake furta wadancan kalamai.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!