Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kaduna

Kaduna: Harin yan bindiga yayi sanadiyyar mutuwar mutane 9

Published

on

Rundunar yan sandan jihar Kaduna ta tabbatar da mutuwar mutane 9 tare da jikkatar mutum guda, sakamakon harin da “yan bindiga suka kai a kauyen Ungwan Dooh (Mado) a karamar hukumar Zangon Kataf.

Wata sanarwa da kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Samuel Aruwan ya fitar, ta ce rundunar Operation Safe Haven ce ta kai rahoton hakan ga gwamnatin jihar Kaduna.

Muna buƙatar ƙarin jamia’n tsaro a Kaduna – El-rufa’i

Aruwan ya ce, cikin gaggawa jami’an tsaron suka amsa kiran zuwa yankin, sai dai tuni maharan suka tsere da ganin sojojin, wanda hakan ne ya bada damar tattara gawarwakin wadanda suka rasa ran su a harin su 9.

Sanarwa ta ce, rundunar Operation Safe Haven ta kuma ceto mutane 12 da suka yi gudun ceton rai, sai dai har yanzu ba a kammala tattara adadin wadanda suka rasa ran su a harin ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!