Labarai
Ba’a Kawo karshen rikicin ja-in ja na mafi karanci albashi ba
Alamu na nuni da cewar har yanzu ba’a kawo karshen rikicin ja-’in-ja kan sabon mafi karancin albashi ba tsakanin kungiyar kwadago da gwamnatin tarayya, kasancewar wasu gwamnoni sun bukaci da a sake nazarin dokar kara albashi.
Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa’I ya ce kamata yayi gwamnatin tarayya ta bar kowacce jiha damar yin sabon mafi karancin albashin dai-dai da aljihun ta da kuma kudaden shiga da take samu.
Gwamnan na Kaduna ya bayyana hakan ne a yayin taron kungiyar gwamnoni ta kasa da ya gudana a jiya a babban birnin tarayya Abuja.
Sauran gwamonin sun hada da na Kwara Abdulfatah Ahmad da shima ya bayyana cewar kamata yayi gwamnatin tarayya ta sakar wa jihohin bara wajen biyan sabon mafi karancin albashin dai-dai ruwa dai-dai-tsaki ganin yadda ake fama da matsalar tattalin arziki.
A dai makon jiya ne kungiyar gwamnoni ta amince da biyan sabon mafi karancin albashi na Naira ndubu 22, da dari 500.
Yayin da a ranar Talata kwamitin sabon mafi karancin alabashi ya mikawa shugaban kasa Muhammadu Buhari rahoto kan sabon mafi karancin albashin yana mai bada shawarar da amince da biyan Naira 30 amatsayin mafi karancin albashin.