Labarai
Babban burinmu daga darajar Kano zuwa matsayin kasashen duniya- Kwamared Waiya

Gwamnatin jihar Kano ta ce, babban burin ta, shi ne daga darajar jihar ya zuwa matsayin kasashen duniya irin su Turkiyya, England, Switzerland da Japan a fanin ayyukan raya kasa da samar da ababen more rayuwa ga al’umma.
Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya bayyana hakan yayin da ya ke ganawa da ƙungiyar Abba Magajin Malam da Ƙungiyar Mawallafan Abba Gida-gida a ofishin sa.
Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya kuma jaddada muhimmancin manufar Kano First Agenda, ya na mai kira ga al’umma da su sanya ci gaban jihar a sahun farko a maimakon bambancin siyasa dake dakile cigaban al’umma.
A nasu jawaban, shugabannin ƙungiyoyin biyu, Alhaji Abubakar Sani da Alhaji Munnir Ibrahim, sun yaba wa gwamna Abba Kabir Yusuf bisa goyon bayan da ya ke ba su, tare da gabatar da wasu buƙatu da za su taimaka musu wajen yaɗa ayyukan gwamnati.
You must be logged in to post a comment Login