Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Babban hafsan sojin kasa ya kaddamar da shirin bunkasa dakarun Operation Hadin Kai

Published

on

Babban hafsan sojin kasa na Najeriya, Laftanar Janar Faruok Yahaya ya kaddamar da wani shiri na bunkasa walwalar dakarun Operation Hadin Kai don kara kyautata harkokin tsaro a kasar nan.

Wannan na cikin wata sanarwa da daraktan yada labaran rundunar Birgediya Janar Onyeama Nwachukwu ya fitar yau.

Sanarwar ta bukaci jami’an da su yi amfani da damar wajen kyautata alaka da sauran sojoji don tabbatar da tsaro da zaman lafiya a kasar nan.

Ta cikin sanarwar, Janar Farouk Yahaya ya ce shirin zai baiwa jami’an damar ziyartar iyalansu da saukaka duk wata zirga-zirga a lokacin gudanar da aikinsu.

An gudanar da bikin kaddamar da shirin ne a jiya a sansanin sojojin sama da ke Maiduguri a Jihar Borno.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!