Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Najeriya ta nuna rashin jin dadinta kan cin zarafin da ‘yan sandan Indonesia suka yi wa jami’inta

Published

on

Gwamnatin tarayya ta nuna rashin jin dadinta kan yadda jami’an ‘yan sandan kasar Indonesia suka ci zarafin wani jami’in difilomasiyyar kasar nan a birnin Jakarta.

Wani faifan bidiyo da aka rinka yadawa ya nuna yadda jami’an hukumar kula da shige-da-ficen Indonesia suka kama jami’in ofishin Jakadancin Najeriya tare da murde masa hannu suna cin zarafinsa yana ihu, suka kuma jefa shi cikin mota.

Wata sanarwa da ma’aikatar kula da harkokin kasashen waje ta fitar, ta ce kamawar da aka yi wa jami’in tare da cin zarafinsa ya saba da dokokin kasa da kasa da kuma yarjejeniyar birnin Vienna.

Sanarwar ta ce Najeriya ta rubutawa Indonesia takardar korafi, tare da gayyato jakadan Indonesia a Najeriya don jin ba’asi, wanda tuni ya nemi afuwa kan faruwar lamarin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!