Labarai
Babban Sifeton yan sanda ya kai ziyara jihar Benue

Babban Sufeton ‘yan sandan Najeriya Kayode Egbetokun, ya kai ziyara jihar Benue ranar Litinin biyo bayan yadda wasu mahara suka hallaka mutane da dama tare da tilasta wasu daruruwa barin gidajensu.
Jihar ta Benue ta dade tana fama da hare-hare da ake zargin makiyaya da kaiwa.
Tsawon shekaru kenan ana wannan kashe-kashen mutane a jihar ta Benue, inda wasu ke danganta matsalar da rikici tsakanin kabilu ko al’ummomin garuruwan da rikicin filaye tsakanin manoma da makiyaya.
To sai dai kashe-kashen na wannan makon sun yi yawa kusan ba kakkautawa, inda aka tabbatar da hallaka wajen mutane 160 a hare-haren da ake zargin makiyaya da kaiwa.
You must be logged in to post a comment Login