Connect with us

Kowane Gauta

Babu abin da ‘yan Najeriya suka mora a gwamnatin Buhari – Gambo Danpass

Published

on

Dattijo Alhaji Gambo Abdullahi Danpass ya kalubalanci gwamnatin shugaban kasa Buhari bisa yadda ya ce gwamnatin ta gaza shawo kan matsalolin da al’ummar Najeriya ke ciki a yanzu.

Alhaji Gambo Danpass ya bayyana haka ne ta cikin shirin kowane Gauta na Freedom Radio Kano, yana mai cewa akwai ayyukan da aka faro a nan Arewacin Najeriya wadanda an kasa kammala su amma na kudancin kasar nan tuni an kammala nasu.

Alhaji Gambo Danpass ya kara da cewa dole gwamnatin shugaban kasa Buhari da sauran mukarraban gwamnatin su sake nazari akan wannan matsalar kasancewar al’amura a Arewacin kasar nan na sake tabarbarewa amma Buhari ya cigaba da zubawa matsalolin idanu.

Yace duk abubuwan more rayuwa sun gagara samu a wannan gwamnatin ta Buhari, dadin da dawa kuma al’amuran cin hanci da rashawa sun dabai baye kowane bangare a gwamnatin.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!