Connect with us

Kowane Gauta

Kada Ganduje ya yi amfani da kudaden Kano lokacin zaben Edo – Al-Amin Al-Barra

Published

on

Kada Ganduje yayi amfani da kudaden jihar Kano lokacin zaben Edo domin dukiyar Kanawa bata ‘yan Edo ba ce- Kwamared Al-Amin Al-Barra.
Kwamared Al-Amin Al-Barra ya shawarci gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da kada yayi amfani da kudaden jihar Kano wajen ganin sun sami nasara a zaben jihar Edo a ranar Asabar mai zuwa domin kudaden mutanan Kano bana ‘yan jihar Edo bane.

Al-Amin Al-Barra ya bayyana haka ne ta cikin shirin kowane Gauta na tashar Freedom radio Kano, yana mai cewa an baiwa gwamna Ganduje jagorancin zaban ne dan yanada kujera a hannunsa ta jihar Kano ne kuma yin adalci shine kadai mafita.

Ya kara da cewa ya zama wajibi su shawarci gwamnan na Kano domin alkalma sun nuna yadda jam’yyun suka dauki zaben na jihar Edo tamkar ko a mutu ko ayi rai don haka ya zama wajibi jami’an tsaro su kara sanya idanu sosai domin ganin anyi zaben cikin kwanciyar hankali da lumana.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 335,158 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!