Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kowane Gauta

Siyasar Kano : Shehu Isah Driver ya yi martani kan kalaman Amanallah Ahmad

Published

on

Babban mataimakin Gwamnan Kano kan kafafan yada labarai Shehu Isah Driver yayi martani kan kalaman Hon Amanallah Ahmad.

Shehu Isa Driver ya kalubalanci kalaman Hon Amanallah Ahmad Muhammad dangane da wata turka turka data faru a lokacin daya shugabanci karamar hukumar Tarauni a shekara ta 2007.

Shehu Isa Driver ya bayyana hakan ne ta cikin shirin kowane Gauta na gidan Radio Freedom Kano, yana mai cewa akwai bukatar Amanallah Ahmad Muhammad ya fito yayi jawabi kan yadda yayi nasara a zaben daya gaba na shugabancin Karamar Hukumar Tarauni kasan cewar ba shine yayi nasara ba a zaben.

Hon Shehu Isa ya kara da cewa tunda shi Amanallah yasan baiyi nasara ba a waccen zabe na 2007 kamata yayi ya tattara duk abundaya samu ya mayarwa da tsohon dan takarar na jam’iyyar PDP da sukayi zabe tare wato Nura Zubairu.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!