KannyWood
Babu adawa tsakanina da Gwamnatin Kano – Naburaska
Jarumin fina-finan Hausa Mustapha Naburaska ya ce babu adawa tsakanin sa da Gwamnatin Kano a yanzu.
Naburaska ya bayyana hakan ne a wata hira da Freedom Radio.
Ya ce, sasancin da suka yi da Gwamnatin ba ƙaramin ci gaba suka samu ba a ɗan ƙanƙanin lokaci, amma hakan ba yana nufin yin siyasa ba, sai dai kawai alaƙar aiki tare da mutunta juna.
Naburaska ya ce, “Gwamnatin baya ba ƙaramar asara ta janyo a masana’antar Kannywood ba, domin kuwa mafi yawan daraktocin masana’antar sun bar jihar Kano zuwa wasu jihohin domin gudanar da ayyukansu”.
Ya ƙara da cewa har kawo yanzu suna samun ƙalubale amma tun da suka gane inda zaren ya ke, suka fara samun sauƙi, domin kuwa a yanzu sun daina bin wata doka ko tsarin shugabancin hukumar tace fina-finai.
Ya ce, kawai dai su na yin abin da suka ga ya fi dacewa.
A don haka ne ma, ya sanya suke yiwa hukumar karan tsaye saboda cewa duk matsalolin da suke samu na da alaƙa da shugabancin hukumar.
You must be logged in to post a comment Login