Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yadda aka rushe ginin jikin masallacin juma’a na Fagge

Published

on

Da safiyar ranar Litinin ne jami’an hukumar tsara birane ta jihar Kano KNUPDA, suka rushe wasu daga cikin gine-ginen da aka yi a masallacin Juma’a na Fagge.

A makon da ya gabata ne hukumar ta bada umarnin dakatar da ci gaba da gini a wurin.

Bada umarnin dai ya biyo bayan umarnin da majalisar dokoki ta jihar Kano ta yi a zamanta na ranar Talatar da ta gabata.

Jami’an hukumar sun isa wurin tare da yin amfani da mota Caterpillar inda suka baje wasu daga cikin ginin.

Tuni dai al’ummar yankin suke ta nuna farin cikin su da tausai ɗin da aka yi a masallacin, duk da jami’an tsaron da aka girke a wajen don hana kwasar ganima.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!