Labarai
Babu baraka a tsakanin Ganduje da shugaba Tinubu- TCC

Kungiyar rajin kare muradun shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu, watau Tinubu Care and Concern TCC, ta ce, sam babu wata baraka da ta kunno kai a tsakanin tsohon shugaban jam’iyyar na kasa Dr Abdullahi Umar Ganduje da shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ko sauran ‘yan jam’iyyar.
Shugaban kungiyar Kamal Sarki, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da kungiyar ta gudanar a Kano.
A cewarsa jita-jitar da ake yada wa wadda ke cewar an kori tsohon shugaban APC din ne ko matsanta masa sauka daga kan mukamin bisa aikata ba dai-dai ba ko samar da baraka a tsakanin ‘yan jam’iyyar inda ya ce hakan ba gaskiya ba ne.
Haka kuma shugaban ya ce, kungiyar ba ta shakkar wata hadakar ‘yan adawa don tunkarar jam’iyyar a babban zabe mai zuwa na shekarar 2027.
You must be logged in to post a comment Login