Connect with us

Labarai

APC ce za ta lashe zaben shugaban kasa a shekarar 2023 – Inji Tinubu

Published

on

Jagoran jam’iyar APC na kasa sanata Bola Ahmed Tinubu ya yi hasashen cewa jam’iyyar APC ce za ta lashe zaben shugaban kasa a shekarar dubu biyu da ashirin da uku.

 

Bola Tinubu ya bayyana hakan ne jim kadan bayan kammala wata tattaunawa da ya yi da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar asorok a jiya talata.

 

Ya ce rade-radin da ake ta yadawa cewa ya samu sabani da shugaba Buhari zance ne kawai da ‘yan adawa ke yadawa da nufin biyan bukatunsu na siyasa.

 

Sanata Bola Tinubu ya kuma soki masu cewa shugaba Buhari dagangan ya ki mai da hankali kan halin rashin tsaro da ke addabar kasar nan, yana mai cewa babu wani shugaba da zai yi biris da harkokin tsaro, ayi ta kashe al’ummar sa babu gaira babu dalili.

 

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!