Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Babu dan wasan Najeriya da ya kwana a karkashin bishiya -Sunday Dare

Published

on

Ministan Matasa da wasanni na kasa Sunday Dare, ya musanta labaran dake yawo cewa, wasu daga cikin ‘yan wasa da masu kula da su na kasar nan sun kwana a karkashin bishiya, yayin wasannin matasa na kasa ‘yan kasa da shekaru 15 da yake gudana a garin Ilorin Jihar Kwara.

Sunday Dare ya ce tun kafin isowar kowacce jiha zuwa gasar sai da aka ware musu guraren kwanan su da sauran abubun da za su bukata.

Ministan ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai jiya Lahadi 17 ga watan Oktobar da muke ciki a garin Ilorin din jihra ta Kwara.

Tun a makon da ya gabata ne dai kafafen yada labarai a Najeriya ke yada labarin cewa ‘yan wasan da suka halarci gasar na cikin mawuyacin hali.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!