Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kasuwanci

Babu mai ikon kara farashin man fetir sai shugaba Buhari – Timipre Sylva,  

Published

on

  • Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur na Najeriya Timipre Sylva, ya ce ba za a yi karin farashin litar man fetir a yanzu ba har sai an kammala tattaunawa da Kungiyar Kwadago.

Timipre Sylva, ya bayar da wannan tabbacin ne yayin da ya ke zantawa da manema labarai a Juma’ar nan a jihar Legas.

A cewar ministan sun samu labarin yadda aka wayi gari da karin farashin man fetir wanda lita daya ya kai naira 212.61.

Timipre Sylva a jawabin nasa ya ce “Ba tare da la’akari da tushen wannan mataki ba, ina so in tabbatar muku cewa sam ba gaskiya bane karin farashin matukar ba shugaban kasa Muhammadu Buhari ko kuma Ministan Albarkatun Man Fetur da muke wakiltar sa ba wanda ya amince da a kara farashin fetur dai-dai da naira guda”.

A don haka ya bukaci jama’a da suyi watsi da batun karin domin kuwa babu dadewa gwamnati tayi wata tattaunawa da kungiyoyin kwadago domin nemo farashi mafi sauki da za a magance tashin farashin danyen mai wanda shi ne ke haifar da karuwar farashin man.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!