Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Addini

Paul Owne: Ni na sace yaran Kano na kaisu Anambra

Published

on

An ci gaba da shari’ar mutanen nan da ake zargi da satar yara ‘yan asalin jihar Kano zuwa jihar Anambra.

Kotun karkashin jagorancin mai shari’a Zuwaira Yusuf Ali ta sanya ranar ashirin da shida ga watan Maris don ci gaba don ci gaba da shari’ar.

Tun farko dai yayin shari’ar, daya daga cikin wadanda ake zargi mai suna Paul Owne ya amsa laifin da ake zarginsa da aikatawa.

Sai dai a bangare guda sauran mutane shidan da ake zarginsu da shi sun kafe kan cewa basu da hannun cikin zargin sace yaran ba.

Daga nan ne kuma alkalin kotun ta ba da umarnin daga shari’ar zuwa ranar ranar ashirin da shida ga wannan wata na Maris.

A nasa bangaren kwamishinan shari’a na jihar Kano Barista Musa Lawal Abdullahi ya ce gwamnatin Kano za ta ci gaba da sa ido don ganin an yi adalci ga iyalen yaran.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!