Labarai
Babu sassauci ga ƴan adaidaitar da ba sa biyan haraji – KAROTA
Hukumar lura da zirga-zirgar ababen hawa ta Kano KAROTA ta ce, babu sassauci ga duk masu baburan adaidaitan sahun da basa biyan harajin da Gwamnati ta sanya musu.
Shugaban hukumar Baffa Babba Ɗanagundi ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da yayi a ranar Laraba.
Baffan ya musanta zargin cewa, hukumar na tilasta wa masu baburan biyan harajin na tsawon watanni maimakon na kullum-kullum.
A cewar sa, ko wane mai Babur zai iya biyan Naira ɗari a kowace rana ba sai ya dunƙule na watanni ba.
A nasa ɓangaren shugaban ƙungiyar direbonin baburan adaidaita sahu na Kano, Sani Sa’idu Ɗankoli ya nemi mammbobinsa da suyi biyayya ga abin da Gwamnati ke buƙata.
Ya ce, yanzu haka suna ci gaba da kira ga Gwamnatin Kano kan ta yi musu sassauci.
Wannan dai na zuwa ne, bayan da matuƙa baburan adaidaitan sahun suka yi zanga-zangar kwanaki biyu kan zargin hukumar ta KAROTA da tilasta musu biyan harajin watanni a lokaci guda.
You must be logged in to post a comment Login