Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Azal: Magidanci ya rataye kansa a Kano

Published

on

Wani magidanci ya rataye kansa a unguwar Sauna Kawaji da ke ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano.

Mutumin mai suna Sabi’u Alhassan mai kimanin shekaru 62 a duniya ya rasu bayan da ya rataye kansa a ranar Laraba.

Rahotonni sun ce, lamarin ya faru ne a lokacin da matarsa ta tafi unguwa babu kowa a gida.

Wakilin Freedom Radio Shamsu Da’u Abdullahi ya halarci jana’izar marigayin da aka yi da yammacin Laraba.

Mutanen unguwar sun shaida masa cewa, basu san musabbabin da ya sanya ya rataye kansa ba.

Mun so jin ta bakin rundunar ƴan sandan Kano amma abin ya ci tura, kasancewar wayar mai magana da yawun ƴan sandan a kashe take.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!