Labarai
Badaƙalar Naira Biliyan 31: ICPC tana neman surikin Buhari ruwa a jallo
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa (ICPC) ta bayyana ɗaya daga cikin surukan shugaban ƙasa Muhammadu Buhari Gimba Ya’u Kumo a matsayin wanda take nema ruwa a jallo sakamakon zargin sa da hannu a badaƙalar dala miliyan sittin da biyar kwatankwacin naira biliyan talatin da ɗaya.
Kumo wanda ya auri ɗaya daga cikin ƴayan shugaba Buhari (Fatima) a shekarar 2016 ana zargin sa ne tare da wasu mutane biyu da suka hada da: Tarry Yusuf da kuma Bola Ogunsola da almundahanar kudaden.
A cikin wata sanarwa da hukumar ta ICPC ta fitar mai dauke da sa hannun mai magana da yawunta Azuka Ogugua, ta yi shelar cewa duk wanda ya san inda surikin shugaban kasar ya ke da ya gaggauta sanar da ita ko kuma ofishin ƴan sanda da ke kusa.
Shidai Gimba Umar Kumo ya rike muƙamin shugaban bankin samar da gidaje ta ƙasa (Federal Mortgage Bank of Nigeria) a lokacin mulkin Goodluck Jonathan.
Ana dai zargin surikin shugaban kasar ne shi da mutanen biyu da karkatar da kudaden hukumar samar da gidaje ta ƙasa da suka kai dala miliyan sittin da biyar.
You must be logged in to post a comment Login