Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Baffa Babba ya nemi afuwar ‘yan adaidaita sahu

Published

on

Shugaban hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano (KAROTA), Baffa Babba Dan Agundi, ya nemi afuwar matuka baburan adaidata sahu.

Baffa Baffa ya ce idan har ya kuntata musu kan matakin da hukumar ta dauka a baya-bayan nan to su yafe masa.

Ya ce a sabanin da aka samu kan batun biyan haraji da rajista ta yiwu wasu da dama sun shiga matsatsi ko kuma sun kuntata.

Muna sane da cewa wasu basu ji dadin yadda muka gudanar da aikin mu ba amma duk abinda muka yi yana bisa doka ” a cewarsa.

Baffa Babba na bayyana hakan ne ta cikin shirin ‘Barka da Hantsi’ na nan Freedom Redio.

A cewarsa yana matukar tausaya masu sana’ar adaidata sahu, har ma ya buga misali da rage kudaden tarar da ake cin su, ta yadda aka tsayar da tarar kar ta wuce naira dubu biyar.

A ka’ida idan mai baburin adaidata sahu ya ajiye shi ba bisa ka’ida ba kamata yayi a cishi tarar naira dubu goma.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!