Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Bahaya a sarari: Ƙananan hukumomin Kano 10 sun fita daga matsalar

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce ƙananan hukumomi 10 sun daina fuskantar Matsalar bahaya a sarari.

Babban sakataren ma’aikatar muhalli Adamu Abdu Faragai ne ya bayyana haka a wani ɓangare na bikin ranar banɗaki ta duniya.

Bikin na wannan shekara ma’aikatar muhalli ta Kano ta gudanar da shi a tashar mota ta Kano line.

Da yake jawabi a tashar Adamu Faragai ya ce “A yanzu mun samu rahoton cewa ƙananan hukumomi 10 a Kano ba su da matsalar Bahaya a sarari cikin ƙananan hukumomi 44”.

Ya kuma lissafo ƙananan hukumomin kamar haka: Madobi, Takai, Gaya, Wudil, Danbata, Garko, Doguwa.

Sauran sune: Sumaila, Kabo, Rano wanda a yanzu basa cikin masu fama da matsalar bahaya a sarari.

Ranar banɗaki: Talauci da ƙaruwar al’umma na haifar da yin bahaya a sarari – Dakta Bashir Getso

Faragai ya ci gaba da cewa yin bahaya a sarari na haddasa cutuka musamman Amai da gudawa baya ga gurɓata muhalli.

“A yanzu mun samar da banɗakuna sama da ɗari huɗu da wanda ƴan kasuwa suka mallaka da kuma na gwamnati, kuma tuni hukumar KNUPDA ta sahale a gina 7 daga ciki” a cewar Faragai.

Ya kuma ce, ma’aikatar muhalli ta samar da banɗakunan tafi da gidanka domin bayarwa a guraren buki ko wani taro da zai haɗa jama’a don sauƙaƙa musu neman wajen biyan buƙata.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!