Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Baiti United ta sayi ɗan wasa naira dubu bakwai

Published

on

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Baiti United FC, dake karamar hukumar Dawakin Kudu ta kammala siyan ɗan wasa Habibu Nura , mai sunan laƙabi Surprise kan Kuɗi Naira Dubu Bakwai.

Habibu, ya cimma yarjejeniyar saka hannu kan Kwantiragi da Baiti United, bayan da ya bar tsohuwar ƙungiyar sa ta Benfica FC.

A wata sanarwa da jami’in hukumar kula da wasanni ta ƙaramar hukumar Dawakin Kudu (DAKUSDA) Abubakar Dawakin Kudu, ya aikewa da jaridar Duniyar wasanni , ta tabbatar da cewar an gudanar da cinikin ɗan wasan ne bisa jagorancin wakilin sa (Agent), da ya cimma yarjejeniya da ƙungiyoyin biyu a madadin ɗan wasan.

Kawo yanzu haka ɗan wasan ya cigaba da ɗaukar horo a sabuwar tawagar tashi don wakiltar ta, a gaba.
@⁨ATR⁩

👆

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!