Connect with us

Labarai

Bani da hannu kan bullar cutar COVID – 19 – Bil Gates

Published

on

Daya daga cikin hamshakan masu kudi a duniya Bil Gates  ya karya ta shi ne ya kirkiri cutar COVID-19.

Bil Gates ya bayyana hakan ne a ya yin da ake zauren tattaunawa da shi ta kafar gidan talabijin na CNN.

An dai ta yada wasu fefen bidiyo dake nanu cewar ana zargin yana da hannu wajen kirkiro cutar don rage al’ummar duniya daga kashi miliyan 15 cikin 100 ta hanyar yi musu riga kafi wanda aka yi ta watsawa ta kafar YouTube.

A cewar Bil Gates gidauniyar sa na zuba kudade masu yawan gaske wajen samar da allurar riga kafi don kare kananan yara daga cututtuka.

Ya ce lokacin da ake tsaka da barkewar cutar an ta kitsa labarukan karya da ba su da tushe-ballantana –makama a harsuna daban-daban da aka ta wallafawa a kafar sada zumunta kan cewa ya amshi wasu makudan kudade wajen yada cutar ta Corona.

Ka zalika Bil Gates y ace duniya ta sheda ya zuba fiye da Dala miliyan dari biyu da hamsin wajen yaki da cutar ta Korona ya yin da gidauniyar  tallafawa alumma na cigaba da zuba kudade wajen inganta harkokin kiwon lafiya a kasashe masu tasowa fiye da 20.

Amma abun takaici ne mutane su juya batun kan cewa ina neman kudi ta wannan hanyar wajen kashe mutane ta hanyar kirkiro cutar Corona

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 330,090 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!