Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Pantami ya kaddamar da ayyukan bunkasa fasaha ta kafar Internet

Published

on

Ministan sadarwa ta kasa Dr, Isa Ali Pantami ya kaddamar da wasu ayyuka da zai bunkasa fasahar sadarwa ta kafar Internet da aka kammala guda 6 a sassan kasar nan baki daya karkashin ma’aikatar sa.

Dr, Isa Ali Pantami ya kaddamar da ayyuaka ne a madadin shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda zai bunksa tare da tallafawa bangaren

Ministan ya nunar cewa gwamnati mai ci na kokarin baza komar tattalin arziki da tabbatar da samar da tsaro da kumwa yaki da cin hanci da rashawa ta hanyar bunkasa fasahar sadarwa don cimma kudurorin ta.

Daga cikin ayyukan da ministan ya kaddamar akwai cibiyar sadarwa a manyan makarantu dake jihar Enugu da ofishin sadarwa da yankin Arewa maso gabashin kasar nan dake jihar Kaduna da cibiyar yada labarai da sadarwa dake jihar Katsina da dai sauran su.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!