Labarai
Bankin duniya ya ce yan Najeriya da ke aiki a kasashen ketare sun aiko dala biliyan 22 a bara
Bankin duniya ya ce, al’ummar kasar nan da ke ayyukan kwadago a kasashen ketare sun aiko da kudade cikin kasar nan da suka kai dala biliyan 22 cikin shekarar da ta gabata.
A cewar bankin Nigeria ce kasa ta daya a nahiyar Afurka kuma ta biyar a duniya wanda al’ummar ta da ke ketare suka turo da kudade kasashen su na asali.
Bankin na duniya ya kuma ce kasar Masar ce ta biyu wanda al’ummar ta mazauna ketare suka turo da dala biliyan 20.
Rahoton na bankin duniyar ya kara da cewa shekarar 2017 ita ce aka fi samun yawan ‘yan kwadago da ke aiki ba a kasashen su na asali ba da su ka turo da kudade mai yawa.
Bankin na duniya cikin rahoton nasa ya kuma ce mafi yawan kudaden
an turo su ne daga Amurka da Turai.