Connect with us

Labarai

Wani kwararren mai bincike ya sha alwashin kwato kudaden gwamnati da aka wawure

Published

on

Wani kwararren mai bincike mai zaman kansa da kwamitin shugaban kasa da ke kwato dukiyar kasar nan da aka sace ya dauko hayarsa, Evangelist Victor Uwajeh, ya sha alwashin shiga lunguna da sakuna na kasar nan domin tabbatar da cewa dukkannin kudade da kadarorin gwamnati da aka wawure sun dawo gareta.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sa wanda aka rabawa manema labarai jiya a Abuja.

Ta cikin sanarwar dai an kuma ruwaito Evangelist Victor Uwajeh na neman hadin kan ‘yan majalisun dokokin tarayya da bangaren shari’a domin samun nasarar shirin.

Evangelist Victor Uwajeh wanda fitaccen mai bincikar kadarorin da aka boye ne na kasa da kasa, ya ce, ya karbi aikin ne domin tallafawa kokarin da shugaba Muhammadu Buhari ke yi wajen kawadda masu ci da gumin al’ummar kasar nan.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,745 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!