Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Bankin Musulunci: An yi babban taro kan haɓaka tattalin arziƙin Najeriya

Published

on

Ƙungiyar Ƴan Najeriya tsofaffin ɗaliban jami’ar musulunci ta Malaysia sun gabatar da babban taro mai taken tsarin bankin musulunci wajen haɓaka tattalin arziƙin Najeriya.

Yayin wannan taro da aka gabatar da ta hanyar fasahar zamani, masana da ƙwararru daga ciki da wajen Najeriya sun gabatar da maƙaloli kan hanyoyin da za a bi domin bunƙasa tattalin arziƙi ta hanyar amfani da tsarin bankin musulunci ba tare da kuɗin ruwa ba.

Baya ga haka an kuma buɗe fagen tambaya ga masana, inda mahalarta taron suka riƙa tambaya ana basu amsa.

Da ya ke jawabi a madadin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari mai magana da yawunsa Malam Garba Shehu, ya jaddada shirin Gwamnatin tarayya na amfani da wannan tsari musamman wajen rabon aikin yi da tallafi ga ƴan ƙasa.

A nasa ɓangaren shugaban bankin musulunci na Taj Bank a nan Najeriya NorFadelizan Abdurrahman ya bayyana amfani da tsarin bankin musulunci a matsayin abin da zai taimaka wajen yaƙi da matsalar tsaro.

Mai Martaba Sarkin Keffin jihar Nassarawa Dr. Shehu Usman Chindo Yamusa shi ne uban wannan taro, ya miƙa saƙon godiyarsa ga mahalarta wannan taro.

Wannan taro da ƙungiyar ƴan Najeriya tsoffin ɗaliban jami’ar musulunci ta Malaysia suka shirya, ya samu halartar manyan jami’an Gwamnati, da malamai da ƙwararru da sauran al’umma da dama.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!