Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kasuwanci

Bankuna zasu fallasa sunayen duk wanda ya saba sabon tsarin canjin kudaden ketare – CBN

Published

on

Babban Bankin Najeriya CBN ya umarci dukkanin bankunan kasar nan da su wallafa sunaye tare da lambar BVN na duk wanda aka samu da sabawa sabon tsari da manufar canjin kudaden ketare.

Rahotanni sun ce CBN ya bayyana hakan ne a cikin wani sakon kar ta kwana da ya aike wa dukkanin bankunan kasar nan.

Haruna Mustafa Daraktan kula da harkokin banki na CBN ya ce an sanar da su cewa akwai wasu daga cikin kwastomomin su da ke yunkurin sabawa sabon tsarin dokar da kuma manufar da bankin ke burin cimma kan canjin kudaden na ketare.

Ya kuma bukaci kwastomomin nasu da su yi biyayya ga sabon tsarin don kauce wa fuskantar rufe musu asusun ajiya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!