Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Badaru ya biya ‘yan Fanshon Jigawa hakkin su

Published

on

Gwamnatin jihar Jigawa a Nigeriya ta ce duk wani ma’aikacin ta da lokacin barin aikin shi ya yi, to ya yi gaggawar shigar da bayanan shi ga hukumar domin karbar hakkin sa na fansho.

Shugaban hukumar a jihar Hashim Ahmad Fagam ne ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da manema labarai a garin Dutsan jihar a ranar 31 ga watan Agusta shekarar 2021.

Ya ce  gwamnati ta biya hakkin ‘yan fanshon da suka bar aiki a watan Yulin wannan shekara kudaden su da ya kai sama da Naira Tiriliyon daya da rabi.

Gwamnatin Jigawa ta rabawa jama’a Awaki domin kiwo

Ya kara da cewa sun bawa iyalan ma’aikatan da suka rasu hakkin su da ya kai sama da Naira miliyan dari biyu da casa’in da biyar.

Hashim Ahmad Fagam ya kara da cewa a yanzu babu wani dan fansho a jihar ta Jigawa da kebin gwamnati hakkin shi da ba’a bashi bah.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!