Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Navy: Za mu samar da ayyukanyi ga al’ummar jihar Kano –AZ Gambo

Published

on

Rundunar Sojin Ruwan kasar nan ta ce, za ta ci gaba da bawa al’ummar jihar Kano guraben aiki a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.

Shugaban Rundunar Chief of Noval staff, Auwalu Zubairu Gambo, ne ya bayyana hakan ta bakin wakilin sa Kwamado Ibrahim Doko Nuraddin, yayin taron wayar da kan al’umma kan muhimmancin tsaro da yadda za su samu damar samun aiki a rundunar da ake gudanarwa duk shekara.

Shugaban rundunar sojin ruwan na Najeriya ta bakin wakilin nasa Kwamado Ibrahim Doko Nuraddin, ya ce sun zabi wayar da kan mutanen Kano ne domin su fahimci yadda aikin rundunar yake.

Wanda hakan yasa suka fara da makarantar Firamaren Gwagwarwa da kwalejin Rumfa dake nan Kano, inda suka rabawa dalibai kayan karatu da suka hadar da littattafai da abin rubutu da gidan sauro da abinci da kuma basu maganin cutar tsutsar ciki.

Kazalika rundunar ta kaddamar da bude aikin da ta yi na samar da rijiyar burtsatse a kwalejin Rumfa.

Ibrahim Dodo Nurraddin a damadin shugaban rundunar na Najeriya AZ Gambo ya ce sun zabi makarantar Firamaren ta gwagwarwa ne duba da cewar yankin ne ya hadar da kabilun dake Najeriya daban daban.

Ya yin taron mai unguwar Gwagwarwa Usman Sunusi cewa yai yana fatan duk wata dama data samu a rundunar za a rinka tunawa da al’ummar jihar Kano musamman ma yankin Gwargwarwa.

Wasu daga cikin daliban makarantar ta gwagwarwa da suka samu tallafin sun bayyan farin cikin su kamar haka.

Danlami Isyaku, shine shugaban makarantar Firamaren gwagwarwa ya bayyana jin dadin shi dangane da zabar makarantar da akai cikin wadan da za’a gudanar da taron

Za dai a shefe tsawon kwanaki biyar ana gudanar da taron a gurare daban daban na jihar Kano

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!