Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Banyi kuskuren barin Barcelona ba zuwa PSG -Messi

Published

on

Dan wasa Lionel Messi ya ce ko kadan bai aikata kuskureba na barinsa Barcelona zuwa tawagar da ke buga gasar  Ligue 1 ta kasar France Paris Saint-Germain ba.

Messi wanda ya koma PSG a matsayin kyauta, sakamakon Barcelona ta gaza sabinta kwantaragin.

Da hakan ya kawo karshen shekarun da ya shafe yana wasa a gasar LaLigar kasar Spain.

Dan wasa Lionel Messi ya taka rawar gani a nasarar da suka samu akan kungiyar da Guardiola ke jagoranta ta Manchester City da ci 2-0 a gasar cin kofin zakarun turai.

Ko kadan banyi kuskuren komawa  PSG ba,” a cewar Messi yayin ganawarsa da jaridar kasar France.

Tun sanda ya koma PSG, Messi kwallo daya ya iya zurawa a wasan da sukai nasara da ci 2-0 a gasar  Champions League a karawa da Manchester City.

Mai shekaru 34 har kawo yanzu ya gaza zura kwallo a gasar Ligue 1.

Haka zalika dan wasa Messi ya lashe gasanni 35 a filin  Camp Nou, ya kuma zura kwallo 672 da kawo yanzu babu dan wasan da ya kaishi yawan kwallo a kungiyar Barcelona da ya bari.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!