Wasanni
Barau FC ta nada Aminu Halilu na Freedom a mataimaki kan yada labarai

Kungiyar kwallon kafa ta Barau FC, tare da mai horar war ta Eugene Agbabe , ta nemi afuwar Dan Jaridar Freedom Radio, Aminu Halilu Tudun Wada, bisa cin zarafin da mai horar war ya yi masa a baya.
Hakan dai ya biyo bayan zaman sulhun da akayi tsakanin mai horar war da Dan Jaridar, bisa cin zarafin sa da mai horar war ya yi mako Biyu da suka gabata ya yin da yake masa tambayoyi bayan kammala wasan kungiyar na gasar firimiyar NPFL ta Najeriya, tsakanin tawagar ta Barau FC da Kun Khalifat FC.
Zaman sulhun da bada hakurin ya gudana ne karkashin jagorancin kungiyar marubuta labaran wasanni ta kasa SWAN reshen jihar Kano, da shugaban ta Zahradden Saleh sai Janar Manaja na kungiyar Barau FC , Mista Dominic Iorfa.
Ya yin zaman Janar Manaja din na Barau FC, ya kara bada hakuri tare da yin kira a yi aiki tare don ci gaban jihar Kano, inda shima mai horar war ya bada hakuri tare da amsa kuskuren da ya yi da ya ce hakan ba zai kara faruwa a gaba ba.
A zaman dai Janar Manaja na Barau FC, Dominic Iorfa ya tabbatar da nadin na dan Jaridar wanda yake ma’aikacin Freedom Radio ne , a matsayin mataimaki na musamman kan yada labarai na mai horar war , da ya ce nadin ya fara aiki ne nan take , Kuma an yi shi ne bisa cancanta da kuma kara kulla kyakyawar Alaka tsakanin kungiyar da Dan Jaridan , da kuma kungiyar SWAN baki daya.
Zaman dai ya kunshi ‘yan jaridu da dama marubuta labaran wasanni na jihar Kano da kasa, sai jami’an kungiyar kwallon kafa ta Barau FC , da masu ruwa da tsaki a harkar kwallon kafa ne suka halarci zaman sulhun da bada hakurin da ya gudana.
You must be logged in to post a comment Login