Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kaduna

Barazanar ɓallewa daga Najeriya ba za ta sa a baku mulki ba – El-Rufa’i ga Igbo

Published

on

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai’I, ya ce, yana goyon bayan mulki ya koma yankin kudancin kasar nan a shekarar 2023, sai dai ya gargadi ‘ƴan kabilar Igbo da su kwana da sanin cewa, barazanar da su ke yi na ɓallewa daga Najeriya ba za ta sa su samu mulki ba.

 

A cewar gwamnan na Kaduna, ita siyasa tana faruwa ne da tattaunawa tsakanin al’ummomi daban-daban don neman ƙuri’unsu.

 

Malam Nasir El-Rufa’I ya bayyana hakan ne yayin wani taro ta ƙafar internet kan harkokin mulki a nahiyar afurka.

 

Inda ya shawarci al’ummar kudu maso gabashin ƙasar nan da su rungumi ɗabi’ar tuntuɓar sauran yankunan ƙasar nan don neman hadin kansu game da zaben na shekarar 2023.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!