Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Barcelona, Man United, Man City, Real Madrid, Juventus, Chelsea, wa ya fi yin abin kunya?

Published

on

Daga Abdullahi Isa

 A bana manyan kungiyoyin kwallon kafa da a al’adance aka saba ganin sun yi kaka-gida, a gasa daban-daban da hukumar kwallon kafa ta tarayya UEFA ke shiryawa, sun kasa kai bantensu a bana.

Masu sharhi kan harkokin wasanni na ci gaba da bayyana mabanbantan ra’ayoyi kan wannan lamari da ya faru a bana, wanda kusan shekaru da dama, ba a ga hakan ya faru ba.

BARCLONA:

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, kungiya ce da ta shahara ba wai a nahiyar turai ba, har ma da duniya baki daya sakamakon sharafin da ta yi tsawon shekarun da suka gabata.

Ko da ya ke Barcelona tauraruwarta ta fara dishashewa a ‘yan shekarun nan sakamakon barin kungiyar da shahararrun ‘yan wasan tsakiyan kungiyar su ka yi, wadanda suka hada da Xavi Hernandez da Andre Iniesta.

A bana Barcelona ta fara wasa da kafar dama, inda ta fara samun nasara a wasanni, sai dai bayan dawowa daga hutun cutar corona al’amura sun sukurkuce ga kungiyar wanda sanadiyyar haka ta rasa kofin Laliga.

Wani abin kunya da ya faru ga kungiyar ta BARCELONA shine shan kashi da ta yi a hannun kungiyar Bayern Munich da ci 8-2 a wasan daf da kusa da na karshe wato quarter final. Wannan wasa dai ya nuna karara cewa kungiyar Barcelona suna ce kawai ya rage amma ba ta cancanci kimarta da ake gani ba a duniya.

MANCHESTER UNITED:

Manchester United kungiya ce da ta shahara a duniya saboda yadda ta yi kaka-gida a gasar firimiyar Ingila da kuma gasar zakarun turai a shekarun baya, to sai dai ta shiga halin tasku bayan da tsohon mai horas da kungiyar Sir Alex Ferguson yayi murabus.

Tun bayan barin Alex Ferguson kungiyar Mancehste United ba ta samu nasarar lashe gasar firimiya ba. Bugu da kari ta sauya masu horaswa akalla guda hudu da suka hada da David Moyes da Louis Vanghal da Jose Mourinho da kuma Ole Gunner Solksjaer.

Wani abin takaici da ya faru ga kungiyar ta Manchester United shine rashin nasara da ta yi a hannun kungiyar Sevilla da ke kasar Spaniya a wasan daf da na karshe a gasar YUROPA.

Ba ko shakka ga duk wanda ya kalli wasan zai sha mamakin yadda kungiyar ta yi rashin nasara duk kuwa da cewa ita ce ta kankame wasan tare da samun damammaki na zura kwallaye a zare, amma sai gashi an tashi a wasa kwallaye biyu a ragarta.

Wannan rashin nasarar shi ya kawo rashin nasara har uku da kungiyar ta yi a bana a gasa daban-daban wadanda suka hada da: Gasar cin kofin Carling da FA da kuma na YUROPA. Haza lika a yanzu ya nuna cewa kungiyar ta shekara uku a jere ba tare da ta lashe ko da kofi guda day aba wanda wannan shine irinsa na farko cikin sama da shekarun 30.

MANCHESTER CITY:

Manchester city kungiya ce da har yanzu ba ta taba lashe gasar zakarun turai ba. Amma magoya bayan kungiyar sun yi zaton bayan sayan kungiyar da wasu larabawa su ka yi daga yankin

gabas ta tsakiya suka kuma kashe makudan kudade, zai kawo karshen wannan matsala, amma sai gashi tsawon shekaru da faru hakan har yanzu dai kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba.

Manchester City ta lallasa kungiyar Real Madrid a wasan kungiyoyi goma sha shida a gasar zakarun turai gida da waje, wanda hakan masu sharhin wasanni su ka yi zato a lokacin ko kungiyar za ta karya waccan bakin tarihi da ta ke dashi a gasar.

Wannan hasashe dai ya kasa cimma nasara bayan da kungiyar ta kwashi kashinta a hannu yayin fafatawa da kungiyar Lyon da ke kasar Faransa. Bayanai dai sun ce kungiyar Mancehster City ita ce kungiyar da ta fi kashe kudade inda ta kashe sama da dala miliyan dari bakwai wajen sayan makamai.

REAL MADRID:

Kungiyar Real Madrid wadda ta fi kowace kungiyar samun nasara a gasar zakarun turai, ta kasa kai bantenta a bana, sakamakon abin kunyar da ta yi na shan kaye gida da waje a hannun kungiyar Manchester city.

Wannan rashin nasarar shi ya kawo karshen kokarin da kungiyar ke yi na sake kafa tarihi a gasar ta zakarun turai.

Duk da cewa Real Madrid ta samu nasarar lashe kofin gasar Laliga amma dama masu sharhin kan harkokin wasanni na ganin rashin dacewar hakan kasancewar anyi ta basu bugun daga kai sai mai tsaron raga da basu dace ba wanda ya taimakawa kungiyar samun nasara.

JEVENTUS DA CHELSEA:

Kungiyoyin Juventus da Chelsea suma dai abin kunyar ta shafesu a bana kasancewar dukkanninsu sun gaza kai bantensu a gasar zakarun turai.

Juventus duk da cewa ta lashe kofin Serie A amma ta kasa kai bantenta a gasar zakarun turai bayan da kungiyar Lyon da ke kasar Faransa ta sai ta mata hanyar komawa gida.

Yayin da a bangare guda Chelsea ta kwashi ruwan kwallaye a hannun kungiyar Bayern Munich.

Sanin kungiyar da ta fi yin abin kunya a bana lamari ne da masu sha’awar wasannin kwallon kafa za su ci gaba da bayyana mabanbantan ra’ayi.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!