Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Kananan hukumomin da Korona tafi Kamari a Kano

Published

on

Gwamnatin Kano ta bayyana cewa kashi 83 cikin 100 na cutar Corona ya fi shafar  kananan hukumomi 10 na jihar.

Babban jami’in kwamitin kar ta kwana na kwamitin yaki da cutar Corona a jihar Kano Dr, Tijjani Hussain ne ya sanar da hakan a ya yin gabatar da rahoto kan cutar Korona a fadar gwamnatin jihar Kano.

Dr, Tijjani Hussain ya ce akasarin kananan hukumomin da suke cikin birnin Kano cutar  ta COVID-19 ta fi shafa ya yin da sauran suka fito daga yankunan karkara.

A cewar shugaban yawan masu dauke da cutar ba zai rasa nasaba da yawan mutane dake zaune a cikin kananan hukumomin cikin birnin Kano ba, kasancewar hakan ya sanya cutar ta yi ta yaduwa

Ya ce daga cikin kananan hukumomin akwai Tarauni da Nasarawa da Fagge da Gwale da Dala da Birni da kewaye.

Sauran su ne Kumbotso da Ungogo da Wudil da kuma karamar hukumar Dambatta.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!