Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Barcelona za ta gabatar da Xavi hernendez a gaban magoya bayanta

Published

on

Kungiyar kwallon ta Barcelona za ta gabatar da Xavi Hernandez a matsayin sabon mai horas da ‘yan wasan ta a gaban dubban magoya bayanta a ranar Litinin 8 ga watan Nuwambar 2021.

Xavi hernendez dai shine zai maye gurbin mai horar da ‘yan wasan kungiyar Ronald Koeman data sallama sakamakon gaza tabuka abin azo a gani da ya yi a kungiyar.

Kungiyar ta shirya bikin gabatar da tsohon dan wasanta a matakin mai horarwa a filin wasa na Nou Camp.

Tuni dai Xavi Hernandez ya saka hannu kan yarjejeniyar shekaru biyu da za ta kare a karshen shekarar 2024.

Xavi dan kasar Sifaniya mai shekaru 41 ya fara horar da Al Sadd tun daga shekar 2019, inda ya amince ya karbi aikin jan ragamar Barcelona a ranar Juma’a 5 ga watan Nuwambar 2021.

Barcelona ta sanar cewa Xavi zai horar da kungiyar zuwa karshen kakar bana daga nan ya kara kaka biyu a gaba.

Xavi, dake tsohon dan wasan kungiyar ta Barcelona ne ya buga mata wasanni 767 ya kuma lashe kofina 25 a shekaru 17 da ya yi a kungiyar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!