Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Kano ce za ta karbi bakuncin gasar wasanni ta Najeriya a 2022 – Sunday Dare

Published

on

Ministan Matasa da wasanni na kasa Sunday Dare, ya ce jihar Kano ce za ta karɓi baƙuncin gasar wasanni ta Najeriya mai taken National Youth Game a shekara mai kamawa ta 2022.

Sunday Dare ya bayyana hakan ne yayin ziyarar da ya kai wa gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje a ofishinsa ranar Asabar 6 ga Nuwambar shekarar 2021.

Ya ce “Wannan shine karon farko da zamu gudanar da gasar a Kano.

Yace “ina cikin jihar Kano lokutan da suka gabata, da hakan ya bani damar halartar gasar Dala Hard Court da aka kammala a jihar,” a cewar Dare.

Dare ya kuma ce sama da Matasa (10,000) ne za su halarci gasar da za ta gudana a jihar, wanda matuka munji dadi da hakan domin kuwa Kano ce jihar da ke da matasa masu son harkokin wasanni kuma cibiyar kasuwanci.

A nasa jawabin gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje godewa ministan ya yi da ya baiwa jihar damar karɓar bakuncin gasar.

Inda ya ce gwamnatin jihar zatayi duk abin da ya dace na ganin ta samar da mahalli mai inganci da za a gudanar da gasar cikin kwanciyar hankali.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!