Barka Da Hantsi
Barka da Hantsi: Tasirin fitar da zakkah da waƙafi ga mahangar tattalin arzikin duniyar musulunci
A cikin shirin na wannan ranar, an tattauna ne kan tasirin fitar da zakkah da waƙafi ga mahangar tattalin arziƙin duniyar musulunchi wajen kawo ƙarshen matsalolin da suka dabaibaye al’umma.
Baƙin da aka tattauna dasu, su ne Injiniya Muhammadu Lawal Maidoki (Sadaukin Sokoto) shugaban hukumar Zakkah da Waƙafi ta jihar Sokoto kuma shugaban gamayyar ƙungiyoyin masu aikin Zakkah da Waƙafi na Najeriya. Sai kuma Dr. Aliyu Ɗahiru Muhammad, Mataimakin shugaba cibiyar nazarin harkokin hada-hadar kuɗi a addinin musulunci ta Jami’ar Bayero Kano, kuma sakatare na gamayyar ƙungiyoyin masu aikin Zakkah da Waƙafi na Najrriya.
You must be logged in to post a comment Login